Afirka ta Kudu ta buƙaci Iran ta fice daga atisayen sojin ƙungiyar BRICS

Ana sa ran za a gama atisayen ranar 16 ga Janairun 2026.
A cewar rahoton, China da Iran sun aika da na’urorin kakaɓar da makamai yayin da Rasha da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) suka tura jiragen yaƙin ruwa, Afirka ta Kudu kuma ta tura jiragen yaƙi ita ma.
Ƙasashen Indonesia, Habasha da Brazil dai sun halarci atisayen a matsayin masu sa ido.
Sai dai an ce jiragen ruwan Iran da suka isa yankin Simon da ke a lardin Western Cape a makon da ya gabata, ba za su ƙara shiga atisayen ba.
Kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Afirka ta Kudu, Kyaftin Nndwakhulu Thomas Thamaha, ya ce atisayen ya fi mayar da hankali a horo na soja ne kawai, wanda ke nuni da ƙudurin ƙasashen na yin aiki tare.
Atisayen ya ƙunshi na yaƙi da ta’addanci da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su domin kare manyan hanyoyin sufurin ruwa da ayyukan tattalin arziki.

