Hukumar harajin Najeriya tace batun dake yawo na cirewa da tura kudi (VAT) ba gaskiya bane.

Hukumar ta ce wannan bayani na yaudara ne kuma babu sabuwar haraji i da aka kafa a kan kwastomomi aka ce wajibi ne sai sun biya.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X.
NRS ta bayyana cewa tun farko dama wannan haraji na aiki a ƙarkashin dokar haraji na Najeriya da aka kafa tun shekaru da dama inda bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi ke cire kuɗin gudanarwa, da na hidima da suka yi da sauran kuɗaden da suke cirewa, ba sabon haraji bane.
Ta bayyana cewa duk wani bayanin da ke cewa gwamnati ta umarci bankuna da su fara cire harajin kashi 7.5 a kan kudin da aka cire ko aka tura da suka kai naira 100,000 ba dai dai bane.
Saboda haka ne hukumar ta buƙaci jama’a da masu ruwa da tsaki da su daina yarda da labaran da ba su da tushe, su kuma dogara ga sanarwar hukumar kai tsaye don sam

