Ƴan bindiga sun kai hari Katsina duk da shirin gwamnati na sakin waɗanda ke tsare.
YAN BINDIGA A KATSINA

Ƴan bindiga sun kai hari Katsina duk da shirin gwamnati na sakin waɗanda ke tsare.

Ƴan bindiga sun kai hari Katsina duk da shirin gwamnati na sakin waɗanda ke tsare.

An sake samun wasu sabbin hare-haren ƴan bindiga a sassan jihar Katsina dai dai lokacin da ake jita-jitar cewa gwamnatin jihar na wani shirin sakin ɗimbin ƴan bindigar da ake tsare da su bayan kamasu a lokuta da dama, sakin da mahukuntan ke cewa na ƙarƙashin yarjejeniyar da aka ƙulla a shirin zaman lafiyar jihar.
Rahotanni sun ce ƴan bindigar sun kai hari kan wata tawagar masu zuwa bikin aure a ƙauyen Unguwar Nagunda da ke ƙaramar hukumar ƙanƙara inda suka kashe aƙalla mutane 2 daga cikin mahalarta bikin a daren Lahadin da ta gabata.
A cewar bayanai, baya ga kisan mutanen 2 ƴan bindigar sun kuma sace mutane 17 ciki har da Amaryar da ake tsaka da bikinta, baya jikkata wasu gommai, kodayake bayanai sun ce 8 daga cikin mutanen da ƴan bindigar suak sace sun kuɓuta tare da komawa ga ahalinsu a jiya Litinin.
Akwai kuma wani harin na daban da ƴan bindigar suka kashe mutum guda a ƙauyen Jaga na ƙaramar hukumar ƙanƙara.
Gabanin wannan sabbin hare-haren ƴan bindigar an jiyo kwamishinan tsaron jihar ta Katsina Nasir Muazu na kare shirin gwamnatin jihar na sakin tarin ƴan bindigar da ke tsare da cewa manufa ce ta samar da zaman lafiya a jihar.
Aƙalla ƴan bindiga 70 da ke fuskantar shari’a kan ayyukan ta’addancin ne bayanai ke cewa gwamnatin jihar ta Katsina ke shirin saki, wanda ta ce manufa ce ta samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Sai dai a jiya Litinin, kwamishinan tsaron ya bayyana cewa babu cikakkun alƙaluman ƴan bindigar da za a saki ƙarƙashin shirin zaman lafiyar.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ƴan bindiga ke kuɓuta daga hannun mahukuntan Najeriyar ba, duk da cewa gwamnatin ƙasar ta sanya hare-haren da suke kaiwa sassan arewa maso yammacin ƙasar a sahun ayyukan ta’addanci.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *