Muna ganin ‘barazana ƙarara’ na harin soji daga Amurka – Shugaban Colombia.

Kalaman nasa na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da shugaba Trump ya ce kai wa Columbiya farmakin sojoji abu ne da zai haifar da kyakyawan sakamako.
A baya dai shugabannin biyu sun yi ta musayar kalaman ɓatanci tsakaninsu.
Sai dai sun yi magana a ranar Larabar data gabat inda suka shirya wani taro a Fadar White House.
A makon da ya gabata ne Amurkan ta kai wa Venezuela hari tare kuma da kama shugaban ƙasar Nicolas Maduro da mai ɗakinsa.

