Karon farko Trump ya amince cewa ƴan ta’adda na kashe Musulmi a Najeriya.

Da ya ke amsa tambaya yayin wata zantawarsa da kafar New York Times a jiya Alhamis, Trump ya bayyana cewa tabbas ya aminta da cewa hare-haren ƴan bindigar da na ƴan ta’adda a sassan Najeriyar na shafar mabiya addinin Islama.
Kafin yanzu Donald Trump ya ƙi aminta da cewa hare-haren ƴan ta’addan na Najeriya kan shafi mabiya addinin Islama, duk da hujjojin da ke fita kan cewa Musulman ne suka fi rasa rayukansu a hare-haren.
Shugaban na Amurka wanda ya jima yana yiwa Najeriyar barazanar kai mata hare-hare gabanin kai harin na ranar Kirsimati, ya ce muddin aka ci gaba da kisan mabiya addinin Kirista ko shakka babu Amurka za ta ci gaba da kai hare-hare.
A cewar Trump tun farko, bisa buƙatar gwamnatin Najeriya ne Amurka ta ƙaddamar da hari a yankin yammacin Najeriyar mai fama da ayyukan ƴan ta’adda.
Trump ya bayyana cewa gwamnatin Najeriyar ta ƙi amincewa da ɗaukar matakan da suka kamata wajen baiwa Kiristoci kariya a sassan ƙasar.
