Yanzu Yanzu : Yan Majalisar Dokokin Rivers sun fara shirin Sauke Gwamnan jihar da Mataimakiyarsa daga Mulkin Jihar

Yanzu Yanzu :Yan Majalisar Dokokin Rivers sun fara shirin Sauke Gwamnan jihar Fubara da Mataimakiyarsa daga Mulkin Jihar.
Yan Majalisar dokoki na jihar Rivers sun fara daukar matakin sauke Gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa, Ngozi Oduh.
A wani zama na majalisa da shugaban majalisar, Martins Amaewhule, ya jagoranta, Shugaban masu rinjaye na majalisar Major Jack, ya karanta sanarwar da ke ƙunshe da zargin matsanancin rashin gaskiya da aikata abubuwa ba bisa ka’ida ba da ake tuhumar Gwamna Fubara.
Sanarwar, wadda ’yan majalisa 26 suka amince da ita, ta zargi gwamnan da aikata abubuwan da ake ganin sun saba wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
Shugaban majalisar, Amaewhule, ya bayyana cewa sanarwar za a mika ta ga gwamnan cikin kwanaki bakwai masu zuwa.
A cikin wannan zama, Mataimakiyar Shugaban masu rinjaye na majalisar , Linda Stewart, ta karanta wata sanarwa ta daban wacce ke ƙunshe da zarge-zargen matsanancin rashin gaskiya da ake tuhuma ga Mataimakiyar Gwamna, Ngozi Oduh.
Wannan ci gaban siyasa alama ce ta yiwuwar shiga wani sabon yanayi na shari’a da siyasa a jihar Rivers, yayin da ake sa ran gwagwarmaya mai zafi a gaba.
TNU tawaito cewa tun bayan da APC ta gargadi Ministan birnin Abuja Nyesom Wike cewa ya cire kansa daga harkokin Siyasar Rivers ko kuma ya sauka daga Kujerarsa ya tafi Siyasa idan ita yafi so.

