AMURKA ZATA DINGA KARBAR GANGAR MAI KIMANIN MILIYAN HAMSIN (50,000,000) DAGA VENEZUELA-TRUMP

A wani sako da ya sanya a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce za a riƙa sayar da man ne a farashin kasuwa – sannan kuma shi zai sarrafa kuɗin inda ya ce, kudin zai amfani al’ummar Venezuela da kuma Amurka.
Hukumomin Venezuelar dai ba su tabbatar da wannan shiri ba.
Tun da farko, shugabar rikon kwarya ta Venezuelar, Delcy Rodriguez, ta ce babu wani dan ƙasar waje da ke mulkin kasarta.

