
Gwamnatin Jihar Kano ta umarci dukkan jamian gwamnati da ke da niyyar tsayawa takara a zaben 2027 da su yi murabus daga mukamansu. Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 24 ga Maris, 2026, wadda Sakataren Gwamnatin Jiha, Umar Faruk Ibrahim ya fitar.
Takardar ta bayyana cewa an dauki wannan mataki ne bisa tanade-tanaden dokar zabe da sauran ka’idojin da ke tafiyar da harkokin ma’aikatan gwamnati. Ta kuma yi nuni da sashe na 88(1) na dokar zabe ta 2026, wanda ya tanadi yadda jami’an gwamnati za su shiga harkokin siyasa tare da tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Hakazalika, an bukaci dukkan wadanda ke sha’awar tsayawa takara da su yi murabus ko su yi ritaya kafin ranar Talata, 31 ga Maris, 2026.
Gwamnatin ta kuma bukaci a yada wannan sanarwa domin kowa ya sani.