Ƴansanda sun kama waɗanda ake zargi da kashe wata mata da yaranta a Kano

A cewar wata sanarwa damai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Lahadi, kamen ya biyo bayan wani samame da jami’an ƴansanda suka gudanar bisa umarnin sufeto janar na ƴan sandan ƙasa Kayode Egbetokun.
Sanarwar ta ce, an kama waɗanda ake zargin ne bayan a wani aiki da aka gudanar da daren ranar asabar17 ga watan Janairu.
Ƴan sandan sun ce bayan binciken farko da aka gudanar wanda aka bayyana a matsayin jagoran ƙungiyar, wanda kuma ɗa ne ga matar da aka kashe, ya amsa laifin sa.
Ya kuma yi bayanin cewa ƙungiyar na da hannu a wasu munanan hare-hare a jihar.
Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin sun hada da tufafi ke jiƙe da jini, da wayoyin hannu guda biyu na wanda aka kashe, da adda, da kulake, da wasu kuɗaɗe da sauran makaman da ake zargin an yi amfani da su a yayin harin.
Rundunar ƴan sandan ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, inda ta ƙara da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

